'Yan Boko Haram sun sace mutane a Kamaru

Dakarun kasar Kamaru Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun kasar Kamaru

'Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a wasu kauyuka biyu dake gundumar Mokolo a arewacin kasar Kamaru suka sace mutane da dama.

Sun kai harin ne dai a ranar Asabar da dare.

Rahotanni sun kuma ce sun kone garuruwan baki daya, mutane uku kuma sun hallaka a yayin da aka yi garkuwa da tarin jama'a.

Kungiyar ta Boko Haram, wadda ta fi karfi a Najeriya, ta kara fadada kai hare-haren a kasashen Chadi da Nijar da Kamaru.

Wannan lamarin ya faru ne a lokacin da dakarun kasar Chadi suka isa kasar domin dafa wa takwarorinsu na Kamaru domin yakar ikungiyar ta Boko Haram.