Internet din Faransa sun tsaya kafin kai hari

Shugaban Faransa Francois Hollande Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane 17 ne suka rasa rayukansu a lokacin da aka kai hari gidan jaridar Charlie Hebdo.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin shafukan sada zumunta na Internet a kasar Farans sun tsaya cik, kwana guda da yin gargadin cewa masu tada kayar baya za su yi kutsen satar bayanai.

Shafukan Le Parisien, da Marianne na daga cikin shafukan da suka samu wannan matsala, duk da cewar daga bisa an gyara.

Gwamnatin kasar Faransa ta ce an yi yunkurin kutsawa shafuka 20,000 dan satar bayanan cikinsu, bayan harin da aka kai babban birnin kasar Paris, da ya hallaka mutane 17.

Sashen da ke kula da shafukan Internet na kasar Faransa yace ya na gudanar da bincike domin gano bakin zaren.

A ranar alhamis din da ta wuce ne, shugaban da ke kula da shafukan Internet a ma'ikatar tsaron Faransa Vice Admiral Arnoud Coustilliere, ya sanar da cewa masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama da ke satar bayanai ta Internet, na da hannu a kutsen da aka yi wa shafukan sada zumunta guda 20,000, sai dai bai yi karin haske kan wannan batu ba.