Ba a yi mana adalci ba - Sojojin Nijeriya

Sojojin Nijeriya a fagen-daga Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Nijeriya a fagen-daga

Sojojin Nijeriya da hukumomin kasar suka kora daga aiki saboda zarginsu da kin bin umarni na yaki da Boko Haram da kuma gudu daga fagen-daga na ci gaba da bayyana irin mawuyacin halin da suka shiga.

A baya-bayan nan dai daruruwan sojoji ne rahotanni ke bayyana cewa aka kora daga aiki, baya ga wadanda aka yanke wa hukuncin kisa bisa zargin kin zuwa yaki da kaurace wa fagen-daga.

Daya daga cikin sojojin a hirar su da BBC ya ce, sojojin suna tserewa ne daga yaki a arewacin maso gabashin Nijeriya ne saboda hukumomin kasar ba su samar masu da kayan aikin da suka kamata ba, suna kuma zargin cewa manyan jami'ansu na tura su fagen-daga ne ana kashe su babu hujja.

Wannan matsalar dai tana tasowa ne a yayinda Tarayyar Afurka ke kokarin tura dakaru don murkushe kungiyar Boko Haram a kasar Kamaru.

Karin bayani