Fada ya sake barkewa a gabashin Ukraine

Birnin Donetsk a gabashin Ukaraine Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Birnin Donetsk a gabashin Ukaraine

Mummunan fada ya barke a birnin Donetsk da ke gabashin kasar Ukraine, musamman a yankin da ke kusa da filin jiragin sama na birnin.

Mahukunatn kasar ta Ukraine sun ce dakarun gwamnati sun maida martani kan mayaka masu goyon bayan kasar Rasha.

An gwabza fadan ne a daidai lokacin da dubunnan mutane ke halartar wani gangamin tunawa da fararen hular da suka mutu a farkon wannna makon lokacin da aka kai wani harin makaman roka kan motar safar da suke ciki a gabashin kasar ta Ukraine.