Hukumomi na kokarin shawo kan cutar murar tsuntsaye a Najeriya

Matattun kaji Hakkin mallakar hoto Arun Lakshman
Image caption Matattun kaji

Hukumomi a Nigeria na ci gaba da fafutukar dakatar da yaduwar cutar murar tsuntsaye da ta bulla a kasar kimanin makwanni biyu da suka gabata.

Annobar dai ta bayyana ne a jihohin Lagos da kuma Kano, inda masu kiwon kaji suka ce suna tafka mummunar asara.

Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna, Kwamishinan aikin gona na Jihar Kano, ya ce matsalar ta shafi gidajen gona 8 a kananan hukumomi 6.

Haka kuma ya ce ana zargin bullar cutar a wasu gidajen gonar 2 a wata karamar hukumar daban.

Ya ce, kawo yanzu hukuma ta san cewar an kashe kaji fiye da dubu 25, amma akwai sama da budu 7 wadanda suka mutu kafin samun rahoton.

Kwamishinan ya ce, wadanda suka bayar da rahoto ne kawai za su samu kudaden diya.