Boko Haram ta na neman zama 'gagarabadau'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekau ya gargadi Kamaru a makon da ya wuce

Harin da kungiyar Boko Haram ta kai a karshen mako a Jamhuriyar Kamaru ya kara nuna cewa kungiyar barazana ce ga wasu kasashen yammaci da tsakiyar Afrika.

Sakamakon harin, gwamnatin Kamaru ta ce mayakan Boko Haram sun sace mutane kusan hamsin yawancinsu kananan yara.

Wannan batu ya nuna yadda mayakan Boko Haram ke fadada ayyukansu, su na kuma neman zama gagarabadau.

Mayakan sun tsallaka iyakar Najeriya zuwa Kamaru tare da kai hari kauyuka biyu da ke yankin Mokolo, inda suka yiwa maza da mata da kananan yara kawanya tare da hallaka mutane uku.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An gona gidaje fiye da 3,000 a Baga

Ministan yada labaran kasar Issa Tchiroma Bakary ya ce "Shammatar mu su ka yi kamar yadda suka saba, sun da kona gidaje 80, sun kuma kashe mutane 3 tare da sace wasu 30-50, ba dai mu tabbatar da adadinsu ba."

A yanzu haka dai, kungiyar ECOWAS na shirin kafa wata runduna ta hadin gwiwa domin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram a yammacin Afrika.