Kamaru ta ceto mutane 24 daga Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption an ceto mutanen ne lokacin da 'yan Boko Haram ke yunkurin tsallaka wa Najeriya.

Rundunar sojin Kamaru ta ce ta ceto mutane 24 cikin kusan mutane 80 da Boko Haram ta sace.

An sace mutanen ne lokacin da mayakan kungiyar ta Boko Haram suka kai hari a kauyen Mabass ranar Lahadi.

Kananan yara da mata na cikin mutanen da aka sace.

Kakakin rundunar sojin kasar, Kanar Didier Badjeck, ya ce "sojin Kamaru sun ceto mutane 24 cikin mutanen da Boko Haram ta yi garkuwa da su a yankin arewa mai nisa".

Ya kara da cewa an ceto mutanen ne a daidai lokacin da sojin na Kamaru suka dirar wa 'yan Boko Haram din lokacin da suke yunkurin tsallaka wa cikin Najeriya.

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau a wani bidiyon ya gargadi shugaban Kamaru Paul Biya a kan cewa zai dunga kaddamar da hari a kan kasar.

Rikicin Boko Haram ya hallaka dubban mutane a Nigeria musamman a arewacin kasar.