'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan yara

Image caption Masu zanga-zangar sun ture wani shingen da aka raba makarantar da filin wasan

'Yan sanda a Kenya sun harba barkonon tsohuwa kan wasu yara 'yan makarantar Firamare a lokaciun da suke zanga-zangar karbe filin wasa da wani dillalin gidade.

'Yan sandan tare da karnukansu sun tarwatsa masu boren da suka hada da yara 'yan shekaru shida a birnin Nairobi.

Hotuna da aka wallafa a shafukan sa da zumunta na Twitter sun nuna yaran na shakewa, yayin da hayakin mai sa hawaye ya turnuke su.

Wani jami'i a kasar ya ce ba za a amince da harba barkonon tsohuwa a kan yara ba kuma ana kuma binciken al'amarin.