Mataimakin gwamnan jihar Niger ya koma APC

Hakkin mallakar hoto AFP AP
Image caption Buhari da Jonathan na takarar shugabancin Nigeria

Mataimakin gwamnan jihar Niger, Alhaji Ahmed Ibeto da wasu masu rike da mukaman siyasa 200 a jihar sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP sun koma APC.

Ibeto ne ya sanarda da sauya shekar a filin jirgin sama na garin Minna lokacin da ya tarbi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari.

Mataimakin gwamnan ya ce ya sauya sheka ne saboda rashin adalcin da ya ce jam'iyyar PDP ta yi masa a zaben fitar da gwani na takarar gwamna a jihar.

Ibeto ya ce "Mun koma jam'iyyar APC saboda an ki yi mana adalci."

Kawo yanzu jam'iyyar PDP ba ta maida martani ba game da sauya shekar.

Wannan matakin zai iya kawo cikas ga jam'iyyar PDP mai mulkin jihar wacce ta tsayar da Alhaji Umar Nasko a matsayin dan takararta na kujerar gwamnan a zaben watan gobe.