'Yan Najeriya sun yi martani kan farashin mai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu 'yan kasar sun ce an rage farashin ne domin shugaba Jonathan ya samu karin kuri'u

Wasu 'yan Najeriya sun yabawa gwamnati saboda rage farashin man fetur, yayin da wasu suka ce ta yi hakan ne domin yakin neman zabe.

A ranar Lahadi ne dai ministar man fetur ta kasar, Mrs Diezani Alison-Madueke ta sanar da cewa an rage kudin man fetur daga N97 zuwa naira N87 kan kowacce lita daya.

A cewarta, sabon farashin zai fara aiki ne daga karfe 12 daren ranar Lahadin, watau ranar 18 ga watan Janairu, 2015.

Sanarwar ta umarci sashen kula da albarkatun mai da kuma kayyade farashin man fetur wato PPRA, ya tabbatar da an bi umarnin.

Wasu 'yan kasar da BBC ta yi hira da su kan batun sun ce hakan abin yabawa ne domin zai rage radadin da 'yan kasar suke fuskanta.

Sai dai wasu sun ce gwamnati ta yi hakan ne domin ta ga alama ba za ta kai-labari ba a zaben da za a yi a watan gobe.

A shekarar 2012 ne dai gwamnati ta kara farashin man feturn din daga N65 zuwa N141, lamarin da ya janyo zanga-zanga a kasar.

Zanga zangar dai ta tilasta wa gwamnati rage farashin zuwa N97.