"Babu adalci a rabon arzikin duniya"

Hakkin mallakar hoto f
Image caption Oxfam ta ce ya kamata a taka wa masu arzikin da ke ci gaba da handama birki

Kungiyar agaji ta Burtaniya, Oxfam, ta ce akwai wagegen gibi game da yadda ake rabon arzikin duniya.

Ta yi gargadin cewa badi warhaka masu arzikin duniya -- wadanda su ne kashi daya cikin dari -- za su kara mallakar arziki fiye da talakawa, wadanda su ne kashi casa'in da tara.

Kungiyar ta Oxfam tana so ne ta fito da wagegen gibin da ke tsakanin masu kudi da talakawa gabanin taron da za a yi na mutanen da suka fi tasiri a duniya a birnin Davos na Switzerland.

Kungiyar ta kara da cewa lokaci ya yi da shugabannin duniya za su taka wa masu kudin da ke da handama birki.

Oxfam ta ce ya kamata a dauki matakin ba-sani-ba-sabo kan mutanen da ke kin biyan haraji, sannan a samar da abubuwan more rayuka da kara labashin ma'aikata.