Wane taron addini aka fi cika a duniya ?

Mutane miliyan shida sun halarci addu’o’in Paparoma a Philippines- Shin za a iya samu samun taro kamar wannan?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu ibada sun taru domin jin hudubar Paparoma Francis a Manila a ranar 18 ga watan Junairu

Mutane akalla miliyan shida ne suka halarci taron addu’o’i a filin Allah ta’ala da Paparoma Francis ya jagoranta a Manila na kasar Philippines a ranar Lahadi.

Hakan ya kafa tarihin na taro mafi yawan jama’a da wani Paparoma ya jagoranta a tarihi.

Shekaru 20 da suka wuce a Manila mutane miliyan biyar ne suka halaci taron da Paparoma John Paul na biyu ya jagoranta.

Ko da yake an samu dandazon jama’a amma bai kai adadin wadanda suka halarci taron addini ba a wasu kasashen duniya. Ga wasu daga cikin tarukan da miliyoyin jama’a suka halarta na addinni a wasu wuraren a duniya.

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Mabiya addinnin Hindu suna wanka a kogin Ganges lokacin ibadar Kumbh Mela a Haridwar a ranar 14 ga watan Afrilun, 2010.

Kumbh Mela – Mutane miliyan 40

Ana bikin ibadar Kumbh Mela sau daya a cikin kowacce shekaru 12, wanda ake cewa shi ne taro mafi yawan jama’a a duniya. Masu ibada sun shiga cikin kogin Ganges lokacin bikin domin wanke zunubansu.

A shekara ta 2001, fiye da mutane miliyan 40 ne suka halarci bikin wankan, wanda ya kafa tarihi a duniya.

A shekara ta 2013, mutane miliyan 30 mabiyar addinin Hindu sun hadu a kogin Ganges da na Yamuna a rana guda. Amma cikin kwanaki 55, mutane miliyan 100 ne suka yi wanka a cikin koguna.

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Musulmi ‘yan Shi’a lokacin bikin Ashura a Iraki a ranar 13 ga watan Disambar 2014.

Addu'ar Arba'in – Mutane miliyan 17

Addu’o’in cika kwanaki 40 a birnin Karbala na kasar Iraki domin jimamin rasuwar Imam Hussein, jikan Annabi Muhammad(SAW).

Cikin shekaru 30 na mulkin Saddam Hussein wanda ke bin akidar Sunna, an haramta bikin arba’in a bainar jama’a a Iraki.

Bayan kifar da mulkinsa, mutane miliyan 17 ne suka halarci bikin a shekara ta 2014 domin addu’ar arba’in ta Imamu Hussein.

Hakkin mallakar hoto Other

Jana’izar Khomeini – Mutane miliyan 10

A ranar 6 ga watan Yunin shekarar 1989 mutane miliyan 10 ne suka halarci jana’izar shugaban juyin juya halin Iran, Ayatollah Khomeini a birnin Tehran.

Aikin Hajji – Mutane miliyan 3

Aikin Hajji a Makka da ke kasar Saudiyya, watau mahaifar Annabi Muhammad (SAW) ana gunadar da shi ne sau daya a kowacce shekara.

Kuma duk Musulmi wanda ke da koshin lafiya da kuma arziki ya wajaba a kansa ya sauke farali ko da sau daya ne a tsawon rayuwarsa.

Hakkin mallakar hoto Other

A cikin shekaru 10 da suka wuce a jere, akalla mutane miliyan biyu ne suke halartar aikin Hajji a Makka a duk shekara.Amma a shekarar 2012 mutanen da suka halarta sun zarta miliyan 3.