Ana gwabza kazamin fada a Sanaa na Yemen

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan ta da kayar baya sun ki kwantar da hankali a Yemen

Ana gwabza fada a Sanaa babban birnin Yemen tsakanin 'yan tawaye na Houthi da kuma sojoji.

An ji karar harbe-harben bindiga a kewayen birnin da kuma karar harba rokoki a fadar gwamnati.

Ministar yada labarai ta Yemen, Nadia al Sakkaf, ta ce shugaban kasar na cikin koshin lafiya, amma birnin na hargitse.

Ta ce "Yanzu haka kungiyoyi uku ke rike da ragamar bangarori daban-daban na birnin, wadanda suka hada da rundunar gwamnati da 'yan tawaye na Houthi da kuma sojoji masu biyayya ga tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh."

Fadan dai na ranar Litinin ya biyo bayan daftarin sabon kundin tsarin mulki da aka wallafa ne wanda kungiyar Houthi ke adawa da shi.