Mali: Lassana ya samu zama dan Faransa

France Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lassana Bathily ya boye wasu mutane ne daga harin wanin dan bindiga

Gwamnatin Faransa, ta baiwa Lassana Bathily dan asalin kasar Mali katin iznin zama dan kasa.

Bathily ya taimakawa wasu mutane ne suka buya yayin da wani dan bindiga ya kai hari a wani babban kantin Yahudawa dake Paris kusan makwani biyu da suka gabata.

Yayin da suke wani bikin mikawa Lassana Bathily katin iznin zama dan kasar, Frai minista Manuel Valls da ministan cikin gida Bernerd Caeneuve sun jinjina irin jarumtakar da Lassana ya nuna a lokacin harin.

Dan shekaru 24, Lassana, wanda ya kasance musulmi ne, ya boye mutane da dama a cikin wani dakin sanyaya kaya domin kada su lalace, inda daga baya ya kira 'yan sanda.