Japan ta bukaci IS ta sako 'yan kasarta

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mr Aba ya ce ba za su daina yaki da ta'addanci ba

Firayi Ministan kasar Japan Shinzo Abe ya bukaci a gaggauta sake wasu Japanawa biyu da aka sace, bayan 'yan kungiyar masu jihadi sun nemi a biya su kudin-fansa.

Ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su tsaya tsayin-daka wajen yakar kungiyar.

Abe ya ce "Barazanar da wannan kungiya keyi ta kashe 'yan kasar Japan, abu ne da ba za mu iya yafewa ba."

A cewar Mr Japan za ta cigaba da aiki da kasashen duniya don samar da zaman lafiya a kasashen da ke fama da ta'adanci kuma kasar ba za ta canza wannan akida ba.

Kungiyar IS ta fitar da wani bidiyo da ke nuna wani dan bindiga rike da wuka, yana tsaye a kan Japanawa biyun, wadanda guda daga cikinsu dan jarida ne, guda kuma wani da ke yi wa sojoji kwangila, wadanda aka sace bara.

Kungiyar ta IS ta bukaci dala miliyon dari biyu a matsayin kudin-fansar mutum biyun.