Ana babban taro kan Boko Haram a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram na neman zama gagarabadau

Manyan jami'ai daga kasashen yammacin Afrika na yin wani taro a Nijar domin tattauna yadda za su hada guiwa wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Ministocin harkokin kasashen waje da na tsaro na kasashen na dubar yiwuwar daukar matakan soji domin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.

Mayakan Boko Haram sun kwace iko da wasu bangarori na arewa maso gabashin Nigeria da kuma kaddamar da wasu hare-hare a Kamaru.

Amurka da Biritaniya da Faransa da kuma kungiyar tarayyar Afrika duk sun tura wakilansu wajan taron.

Ministan harkokin wajen Nijar, Muhammad Barzoum, ya ce hare-haren kungiyar Boko Haram na bukatar hada kai domin daukar mataki na bai daya.

Chadi ma wacce ta tura wakili, kwana-kwanan nan ta aika dubban dakaru zuwa arewacin Kamaru don dakile hare-haren Boko Haram, bayan da aka sace mutane 80 a karshen makon jiya.