Boko Haram: Muna ba da hadin kai Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram tana fadada kai hare hare zuwa tsallaken iyakoki

A Najeriya, hukumomi a kasar sun musanta cewa ba sa bayar da hadin kai ga sauran makwabtan kasashe wajen yaki da ta'addanci.

Shugaban cibiyar samar da bayanai game da yaki da ta'addanci a Nigeria, Mista Mike Omeri ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta dukufa wajen kawo karshen hare-haren kungiyar Boko Haram.

Ya ce gwamnatin ta kuduri aniyar samar wa sojojinta makamai domin tunkarar mayakan kungiyar.

A cikin watanni 18 da suka gabata, an yi kiyasin mutane dubu biyar ne suka mutu sakamakon hare-haren kungiyar ta Boko Haram, ya yin da dubu 750 suka gudu daga gidajensu.