An soki amfani da na'urar Range-R a Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sanda na leken gidajen mutane da na'urar Range-R ta cikin bango

An fara sukar wani tsarin fasahar zamani wanda ke bai wa jami'an 'yan sanda damar leko cikin gidajen mutanen da suke zargi da aikata laifuffuka.

Kimanin jami'an 'yan sanda 50 ne a Amurka aka tanadar wa na'urar da zata iya aika wa da bayanai ta cikin bangon gine gine.

A bara ne labarin na'urar mai suna Range-R ya fito fili, a wata kotun Denver.

'Yan sanda na yin amfani da na'urar ce wajen sake cafke masu laifin da suka karya yarjejeniyar sakinsu da aka yi.

A wata shari'a a gaban kotu, lauyan dake kare wani Steven Denson ya kalubalanci jami'an tsaro ko suna da hurumin shiga gidansa.

Koda yake alkalai sun nuna dacewar bincike da tuhumar da aka yi wa Denson, sun ce basa tababa a kan na'urar Range-R zata haifar da tambayoyi daga jama'a.

An fara kirkiro na'urar ce a Amurka domin taimaka wa sojojin Amurka dake yaki a Afghanistan da Iraki, sannan daga baya hukumomin tsaro suka ga tana da amfani a wurinsu.

A shekarar 2001, kotun kolin Amurka ta yanke hukuncin hana 'yan sanda yin amfani da na'urorin daukan hoto a gidajen mutane batare da sun samu amincewar yin haka ba.