Burtaniya ta fi kowace kasa sakin bayanai

Britain Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Burtaniya ta fi sake bayanai domin amfanin al'uma

Wani bincike ya nuna cewa Burtaniya ta fi kowace kasa sakin bayanai a duniya ga 'yan kasarta.

Sai dai Sir Tim Berners-Lee dake hada shafukan intanet, wanda kuma kamfaninsa ya gudanar da binciken ya ce akwai sauran tafiya ga kasar.

Akalla kasashe 86 aka yi nazari a kansu kan yadda gwamnatin kasashen ke bari a yi kididdigar bayanan kasar.

Kasar Amurka ce ta zo ta biyu yayin da Sweden ta zo ta uku.

Sir Tim har ila yau ya soki gwamnatoci da dama saboda gazawa da suka yi na kin cika alkawuran fitar da bayanai domin amfanin al'uma.

Ya bayyana cewa kashi 90% ciki 100 na kasashen da aka duba ba sa bari a samu bayanan da suka shafi cin hanci da rashawa.

"Akwai kasashe da dama da suka yi alkawari fitar da bayanan masu muhimmanci, amma da yawa daga cikin su ba su cika alkawari ba. In ji Sir Tim.

Kasar Kenya ta na mataki na 27 wajen fitar bayanai kamar yadda binciken ya nuna.