'Yan tawaye sun kwace fadar shugaban Yemen

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana zaman dar-dar a birnin Sanaa

'Yan tawaye mabiya Shi'a a Yemen suna harba rokoki a kan fadar shugaban kasar, Abdrabbuh Mansour Hadi, a Sanaa babban birnin kasar.

Wani jami'in gwamnati ya ce shugaban na cikin gidan nasa, amma yana cikin koshin lafiya.

Harin na zuwa ne bayan 'yan shi'ar sun karbe ikon wani gidan gwamnatin da ke birnin.

Hakim al-Masmari, babban edita ne na jaridar kasar, ga abinda yake cewa sa'o'i kadan da suka wuce, "A yanzu haka dai fiye da tankokin yaki 280 da manyan makaman da ake harbawa daga nesa naduk suna hannun Huthis. An kuma kashe mutane da yawa."

Yanzu haka dai kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya na wani taro a asirce kan rikicin na Yemen.