Ku karbi katin zabe, ku kare kuri'unku - Buhari

Hakkin mallakar hoto apc
Image caption Buhari ya ce a zabi APC Sak

Dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar APC ta Najeriya, Janar Muhammadu Buhari ya bukaci magoya bayansa su tabbatar sun karbi katunansu na zabe domin kada masa kuri'a.

A lokacin da je yakin neman zabe jihar Kano ranar Talata, Janar Buhari ya ce, "idan baku karbi katunan zabe ba, taruwar da kuka yi anan ba ta da mafani. Ba za ku iyar zabenmu har mu taimaka muku, mu taimaka wa kasarmu ba."

Dan takarar jam'iyyar ta APC ya kara da cewa "idan kun kada kuri'unku, ku kasa, ku raka, ku tsare, ku jira. Ku zabi APC Sak."

Shi ma Janar Buhari ya saka jar hula ta alamar kwankwasiyya a Kano.

Dubban magoya bayan Janar Buhari ne dai suka tarbe shi a birnin na Kano.