Faransa za ta dauki matakai kan ta'addanci

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Manuel Valls

Firayi ministan Faransa, Manuel Valls ya sanar da sabbin matakan tsaro sakamakon hare-haren da 'yan bindiga suka kai Paris makonni biyu da suka gabata.

Lamarin ya janyo mutuwar mutane 20 wadanda suka hada da maharan su uku.

Da yake jawabi a fadar Elysee, Firayi ministan ya ce za a dauki sabbin ma'aikatan leken asiri fiye da 2680 nan da shekaru uku don bincike a kan masu tsattsaurar akida.

Ya kara da cewa yanzu haka a Faransa fiye, da mutane 1300 ake zargi da hannu a kungiyoyin masu jihadi, kuma za a cigaba da bibiyarsu.

A cewar Mista Vall, gwamnatin Faransa za ta kashe kudi kimanin dala miliyan 500 don kare barazanar ta'addanci.