Kamaru ta ceto Bajamushe daga Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM
Image caption Boko Haram ta sace Bajamushen ne a watan Yuli

Gwamnatin Kamaru ta ce ta kwato Bajamushen da kungiyar Boko Haram ta sace kwanakin baya.

A cewar gwamnatin an kwato Bajamushen ne bayan wani farmaki da dakarunta da na kawayenta suka kai wa 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Kungiyar ta ce Bajamushen ne a watan Yulin da ya gabata a arewacin kasar.

Ba a bayar da cikakken bayani kan yadda aka ceto shi ba.

Bajamushen malamin makaranta ne a kasar ta Kamaru.