Za a halasta ta'ammali da wiwi a Jamaica

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An shafe shekaru da yawa ana tafka muhawara a kan cire hamci kan tabar wiwi

Majalisar ministocin kasar Jamaica ta amince da wani kudurin doka da zai halasta wa jama'a a kasar yin ta'ammali da tabar wiwi.

Hakan yana nufin a karon farko, masu bin al'adun Rasta a kasar, wadanda ke yawan amfani da magungunan gargajiya, za su samu damar shan tabar wiwin batare da takura ba.

Ministan shari'a na kasar zai gabatar da kudurin ga majalisar dattijan kasar domin ta amince da shi zuwa doka.

Dokar zata samar da hukumar lura da noman tabar wiwin a kasar, da sayar da ita, da kuma safararta zuwa wasu wurare domin yin maganin wasu cututtuka.

An shafe shekaru da yawa ana tafa mahawara a game da bukatar yin sassauci ga dokar data haramta ta'ammali da tabar wiwi a kasar.