WhatsApp ya fara aiki a kwamfutocin ofis

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kimanin mutane miliyan 700 ne ke amfani da WhatsApp a duniya

Shafin sada zumunta na WhatsApp ya sanar da cewa yanzu mutane zasu iya aikawa da sakonni ta shafin daga kwamfutocin da ake aiki da su a cikin ofis.

A sanarwar da ya bayar ta shafinsa na intanet, kamfanin WhatsApp ya ce mutane zasu iya ganin sakonnin da aka aika ta kwamfutocin a wayoyinsu na salula.

Sai dai masu amfani da kwamfutocin dake aiki da manhajar IOS ta Apple ba zasu samu damar amfani da WhatsApp din a kwamfutocin ba.

Kamfanin WhatsApp ya ce "ba za mu iya samar da hanyar amfani da WhatsApp a kwamfutocin ofis masu manhajar IOS ba saboda tsaurin da IOS din ke da shi".

A watan Fabuwairun bara, kamfanin shafin sada zumunta na Facebook ya saye WhatsApp a kan kudi dala biliyan 19.

A kwanakin baya kamfanin ya bayar da sanarwar cewa masu amfani da shi a wayoyin salula sun kai miliyan 700.

Shafin sada zumunta na WhatsApp ya na daya daga cikin manya manyan hanyoyin aikawa da sakonni a duniya.

A yanzu, kamfanin yana cajin mutane Santi 99 ($0.99) a shekara, bayan sun cinye garabasar amfani da shi kyauta na tsawon watanni 12.