Chadi na da alaka da Boko Haram – Dasuki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dasuki ya ce Chadi na goyon bayan Boko Haram

Babban mai bai wa shugaban Nigeria shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki ya yi zargin cewa hukumomi a kasar Chadi suna da dangantaka mai karfi da shugabannin kungiyar Boko Haram.

Dasuka -- wanda ya bayyana haka a wani taro kan tsaron Nigeria a London -- ya ce a kokarin murkushe ayyukan Boko Haram dakarun Chadi za su shigo cikin Nigeria domin taimakawa wajen yaki da kungiyar.

A cewarsa, akwai matsorata a cikin dakarun Nigeria wadanda ba suda kwarin gwiwar tunkarar yaki da Boko Haram.

Kanar Dasuki ya kara da cewar dakarun Nigeria na da cikakkun makamai kuma bidiyon da Shekau ya nuna da makaman da Boko Haram ta kwace a garin Baga na jihar Borno alama ce da ke nuna cewa sojojin kasar na da makamai masu yawa.

Sannan kuma mashawarcin na musamman ga Mr Jonathan ya ce za a samarda tsaro sosai domin gudanar da zabukan watan Fabarairu.