Kamfanin eBay zai rage ma'aikatansa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamfanin eBay yana shirin rage ma'aikata 2400

Katafaren kamfanin hada hadar kasuwanci ta intanet a Amurka, eBay ya na shirin rage ma'aikatansa 2400 a cikin watanni uku na farkon shekarar 2015.

Yunkurin rage kashi 7 cikin 100 na ma'aikatan eBay ya zo ne a daidai lokacin da kamfanin ke shirin ballewa daga tarayya da tsarin biyan kudin ciniki na PayPal a wannan shekarar.

Kamfanin na eBay ya sanar da hakan ne a cikin rahoton cinikinsa na karshen shekarar bara.

Kamfanin ya ce manufar rage ma'aikatan ita ce domin ya samu sukunin sake inganta ayyukansa da tabbatar da samun cigaba.

Haka zalika, kamfanin na eBay ya ce ya kulla wata yarjejeniya da wani dan kasuwa mai rajin kare hakkin jama'a, Carl Icahn, domin bai wa masu zuba jari iko da tsarin PayPal, bayan sun rabu a tsakiyar wannan shekara.