Ministoci za su yi taro a London kan IS

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ministocin za su duba yadda za a kara taimakawa wadanda rikicin IS ya ritsa da su

Ministocin kasashen waje 21 za su hallara a London a ranar Alhamis domin tattauna yunkurin da duniya ke yi na kawo karshen kungiyar IS.

Taron na son ya dakatar da daukar mayaka da kungiyar take yi tare da hana ta samun kudade da kuma hana ta yada akidojinta.

Haka kuma kasashen za su duba yiwuwar taimakawa wadanda ke yaki da kungiyar ta IS kamar Kurdawa ta fannin soji.

Turkiyya dai ta ce ta kasa dakatar da 'yan kasashen wajen da ke ketara bakin iyakarta zuwa Syria domin yaki tare da kungiyar ta IS.