Shugaban kungiyar PEGIDA ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lutz Bachmann ya bayyana masu gudun hijira a matsayin dabbobi

Daya daga cikin jigajigan kungiyar PEGIDA wadda ke jagorantar zanga zangar kin jinin addinin musulunci a Jamus ya yi murabus a matsayin shugaban kungiyar.

Lutz Bachmann ya kuma bada hakuri a game da rubuce rubucen da ya yi a shafinsa na Facebook, a inda ya kira masu neman mafaka a matsayin dabbobi marasa daraja.

Murabus din ya zo ne bayan masu shigar da kara na gwamnati sun fara shirin tuhumar sa da neman haddasa fitina.

Mista Bachmann ya sanya hotonsa a intanet, inda ya nuna kama da Adolf Hitler, da kwatanta masu gudun hijira da dabbobi.

Kimanin mutane dubu 10 ne suka halarci zanga zangar nuna kin jinin addinin musuluncin a Leipzig, adadin da ya yi kasa da dubu 40 da suka sa rai.