Sarki Abdallah na Saudi Arabia ya rasu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sarki Abdallah ya rasu bayan ya yi jiyya a wani asibiti a Riyadh

Sarki Abdallah Bin Abdulaziz na kasar Saudi Arabia ya rasu.

Sarkin ya rasu yana da shekaru 91, bayan ya yi fama da ciwon sanyin hakarkari.

Gidan talabijin na kasar ya bayyana cewa sarkin wanda tun watan Disamba aka kwantar da shi a asibiti ya rasu a daren Juma'ar kasar Saudiyya.

An yi jiyyar sarkin ne a wani asibiti a babban birnin kasar, Riyadh, sakamakon cutar ta nimoniya(Pneumonia).

Yarima mai jiran gado, Salman Bin Abdulaziz Al Saud ne zai gaji marigayin.

Al'ummar kasar sun fara zaman makokin rasuwar Sarkin.