Dakarun Ukraine sun janye daga filin jirgin sama

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rikicin ya hallaka mutane 5,000 a Ukraine

Bayan kwashe watannin ana gwabza fada, rahotannin sun ce dakarun gwamnatin Ukraine sun janye daga tsakiyyar filin jirgin saman birnin Donetsk da ke gabashin kasar.

Filin jirgin saman muhimmin wuri da 'yan aware masu goyon bayan Rasha ke kai ma harin akai-akai.

Kakakin sojan Ukraine Andriy Lysenko ya ce "Ukraine ta dora wa 'yan awaren laifin kai wani hari kan wata doguwar motar Bus a birnin Donestk da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane takwas."

Firaministan Ukraine Arseniy Yatsenyuk ya ce Rasha ke da alhakin wannan aikin da ya kira na rashin imani.

Kungiyar wanzarda tsaro da dadin a nahiyar Turai OSCE, ta ce a yanzu akalla mutane dubu biyar sun hallaka a cikin fadan wanda ya soma watanni tara da suka wuce.