Shugaba Abdurrabu Hadi na Yemen ya yi murabus

'Yan tawayen Houthi na Yemen Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan tawayen Houthi na Yemen

Shugaban Yemen Abdurrabbu Mansour Hadi da Majalisar ministocinsa sun yi tayin yin murabus domin nuna rashin jin dadi game da kwace iko da Sana'a babban birnin da yan tawayen Houthi suka yi.

Sai dai rahotanni sun ce majalisar dokokin kasar ta ki amincewa da murabus din nasu, to amma Shugaba Hadi ya ce ba zai iya ci gaba da shugabancin ba bayan da aka cimma kiki -kaka a shawarwari tare da yan tawayen.

Wani Shugaban yan Houthin yayi marhabin da shawarar ta Shugaba Hadi sannan ya kawo shawarar kafa wata majalisar shugaban kasa domin cike gibin siyasar.

Har yanzu dai 'yan tawayen ba su janye daga gidan Shugaba Hadi da kuma fadarsa da suka mamaye ba; duk da alkwalin da suka yi na yin hakan a cikin wata yarjejeniya da aka cimma da nufin kawo karshen kiki-kikar da ake yi a birnin na Sana;a.

Haka ma 'yan tawayen ba su sako wani babban jami'in fadar shugaban kasar da suke garkuwa da shi tun a makon jiya ba.