An jefi ministan Abuja a Bauchi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An jefi ministan ne lokacin yana jawabi

Wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun jefi ministan Abuja, Bala Mohammed lokacin yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan a birnin Bauchi.

Ministan dai yana jawabi ne, sai kawai wani da ke cikin taron ya jefe shi da ledar ruwan da ake kira "pure water".

Kodayake jifan ya ba shi mamaki, amma Bala Mohammed ya ci gaba da jawabinsa, kuma kafin ya gama sai aka sake jefo wani abu a kusa da shi.

Ko a Katsina ma sai da wasu matsa suka jefi tawagar shugaba Goodluck Jonathan a lokacin da ya je yakin neman zabe jihar.

Tuni dai kungiyoyi masu sa ido kan siyasa suka fara kira ga 'yan siyasa su ja hankalin magoya bayansu don kaucewa tayar da hankali a lokacin yakin neman zabe.