'Boko Haram: Ana yi wa mata fyade a Baga'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram sun yi matukar barna a Baga

Wata mata da ta samu kubuta daga garin Baga wanda ke karkashin ikon kungiyar Boko Haram ta yi wa BBC bayanin irin halin da suka shiga ciki a garin.

Matar ta yi zargin cewa 'yan Boko Haram na yi wa mata fyade tare da azabtar da mutane.

A cikin hirar ta ce "Yanzu 'yan Boko Haram ne ke iko da mata a garin Baga, Doron Baga, Mile 3 da kuma Mile 4. Suna yi wa 'ya'yanmu fyade suna cin zarafin mutane."

Ta kara da cewar "Sun fasa shaguna sun kwashe kayan abinci, sun kona mana gidaje. Ba sa yarda 'yan mata sun fita daga gidajensu."

"Suna tilastawa mata birne gawawwaki, sannan suna yi wa mutane wa'azi da safe da kuma yamma," in jin matar da ta kubuta.

A farkon wannan watan ne 'yan Boko Haram suka kwace garin Baga inda suka hallaka mutane da wasu suka kiyasta a matsayin kusan 2,000.

A halin yanzu dubban 'yan Baga da Doron Baga ne ke zaman gudun hijira a sansanonin da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno.