Brazil na fuskantar fari

Shugabar kasar Brazil Dilma Roussef Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Baya ga matsalar fari, Brazil ta dade ta na fuskantar koma bayan tattalin arziki.

Ministar muhalli a kasar Brazil Izabella Teixeira ta ce yankin kasar da ya fi kowanne yawan jama'a na fuskantar mummunan fari da ba a taba gani ba tun shekarar 1930.

Miss Teixeira ta bukaci mazauna jihohin Sao Paulo, da Rio de Jenairo da Minas Gerais su yi tattalin ruwan amfanin yau da kullum, inda ta bayyana halin da ake ciki da cewar mummuna ne kuma mai tada hankali.

Yawancin kananan hukumomin jihohin Brazil sun fara tattalin ruwan na su, haka kuma an yi hasashen cewa rashin ruwan zai shafi masana'antu da ayyukan noma, da kuma girgiza tattalin arzikin kasar.

Haka kuma Farin zai shafi wutar lantarki daga madatsun ruwan da ake samar da yawancin wutar lantarkin kasar.