Ba za mu jinkirta lokacin zabe ba – INEC

Image caption Hukumar ta ce ba za ta dage lokacin zabe ba

Hukumar zaben Najeriya ta ce tana da kwarin gwiwar kammala bai wa 'yan kasar katunan zabe kafin a yi zabukan 2015.

A ranar Alhamis ne dai babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki, ya ce ya bai wa hukumar zaben shawara ta dade zabukan saboda har yanzu mutane miliyan 30 ba su karbi nasu katunan ba.

Sai dai kakakin hukumar zaben -- Kayode Idowu -- ya ce za su kammala bai wa 'yan kasar katunan zaben kafin karshen watan Janairu.

Ya kara da cewa suna daukar matakai domin tabbatar wa 'yan gudun hijirar da hare-haren Boko Haram suka raba da gidajensu sun yi zabe.

Mutane fiye da miliyan 68 ne suka yi rijista domin kada kuri'a a zabukan kasar na watan Fabarairu.