Dattijuwa mai shekaru 90 ta koma karatu

Image caption Dattijuwa Priscilla tare da abokan ayyukansu

An yi amman cewa wata dattijuwa mai shekaru 90 a duniya da ta koma karatu tare da tattaba-kunnenta shida, ita ce ‘yar makarantar Firamari da ta fi kowanne yawan shekaru a duniya.

Priscilla Sitienei na zaune a teburin da ke gaba a ajinsu sanye da rigar makaranta kuma ta kasa kunne sosai, yayin da take rubuta sunayen dabbobi da turancin Ingilishi a littafinta.

Ta shiga makarantar Leaders Vision Preparatory ne shekaru biyar da suka wuce ne, kuma ta shafe shekaru 65 a matsayin ungozoma a kauyenta na Ndalat da ke Rift Valley.

Hasalima dai ta yanke cibin wasu daga cikin abokan karatunta masu shekaru 14 da kuma 10.

Gogo kamar yadda aka fi kiranta a harshen Kalenjin ta ce ga shi a yanzu tana iya karatu da rubutu yayin da take da shekaru 90 a duniya, damar da bata samu ba a lokacin da take karama.

Tafi jin dadin magana da harshenta na Kalenjin fiye da turanci, kuma ta yi karin bayani kan dalilan da suka sa ta koma makaranta.

“Ina so in dinga karanta littafin Linjila, kuma ina so in zama wata babbar misali ga yara wajen zuwa makaranta.

Yaran da suka girma da dama wadanada ma ke da nasu ‘ya’yan ba sa zuwa makaranta.”

Gogo ta ce ta kan sa yara a gaba ta tambaye su me yasa ba sa zuwa makaranta.

Sai su ce mini wai su sun girma da karatu, sai in ce musu ni ina zuwa makaranta saboda haka kuma ya kamata ku koma makaranta.”

Da fari dai makarantar ta ki daukar Gogo, amma daga bisani da suka lura da gaske take sai suka amince.

Shugaban makarantar, David Kinyanjui ya yi amanna Gogo wacce ke zaune a kauyen da makarantar take kyakkyawar misali ce ga sauran ‘yan ajinta.

Ya ce “Duka dalibai suna sonta, kuma suna son yin wasa da ita.”

A yanzu dai Dattijuwar na da mukami a cikin dalibai kuma tana halartar aji domin koyon darussan lissafi da turanci da motsa jiki da rawa da waka da kuma wasan kwaikwayo.

Sanye da shudiyar rigar makaranta, Gogo kan bai wa sauran ‘yan ajin da take labarai a karkashin bishiyar da ke kusa da filin wasa, don tabbatar da cewa sun amfani daga abinda ta sani na al’adunsu.