Gwamnatin kasar Yemen ta yi murabus

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Abdrabbuh Mansour ya ce ba zai iya ci gaba ba saboda 'yan tawaye

Shugaban kasar Yemen Abdrabbuh Mansour da mukarabansa sun mika takardunsu na yin murabus, a wani mataki na yin bore ga karbe babban birnin Sanaa da 'yan tawayen Houthi suka yi.

Mista Mansour ya ce babu yadda za a yi ya ci gaba da mulkar kasar bayan da aka kasa cimma shirin tsagaita wuta da 'yan tawaye.

Masu sharhi sun ce murabus din shugaban kasar da mukarrabansa a lokaci guda, wani abu ne da ba wanda ya tsammanin zai faru.

'Yan tawayen dai sun nuna gamuswarsu da murabus din shugaban, suna masu kira da a kafa wani kwamiti dai zai ci gaba da gudanar da harkokin kasar.