Boko Haram ta kashe mutane 12 a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM
Image caption Hare-haren na faruwa ne a daidai lokacin da shugaba Jonathan ke yakin neman zabe a Borno

Mazauna Konduga da ke jihar Borno a Najeriya sun ce 'yan Boko Haram sun kashe mutane 12 lokacin harin da suka kai musu.

'Yan kungiyar ta Boko Haram sun kai hari ne a kauyen Kambari da ke karamar hukumar ta Konduga ranar Alhamis da yamma.

Shaidu sun fada wa BBC cewa an kona wasu sassa na kauyen.

Sun kara da cewa an kai harin ne lokacin mutanen garin sun tafi cin kasuwar wani kauye da ke kusa da su, don haka yawancin mutanen da aka tsofaffi ne.

Wannan lamari na faruwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Goodluck Jonathan ke kai yakin neman zabe a jihar a ranar Asabar.

Dubban mutane kungiyar ta Boko Haram ta kashe a jihar, kuma har yanzu gwamnati ba ta shawo kan kashe-kashen ba.