Babu bukatar a dage zabe - INEC

Zabe a Nijeriya Hakkin mallakar hoto b
Image caption Zabe a Nijeriya

Hukumar zaben Nijeriya, ta ce, ba ta bukatar a dage zabe daga watan Fabrairu mai zuwa, domin a shirye take ta gudanar da babban zaben.

Mai magana da yawun hukumar, Mista Kayode Idowu wanda ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da sashen turanci na BBC, ya ce hukumar za ta kammala rarraba katunan zabe na din-din-din ga 'yan kasar kafin ranar zaben.

Yace a cikin katuna miliyan 52 da hukumar ta buga ta kuma fito da su don raba wa a ranar bakwai ga watan Janairu, miliyan sha-biyar kawai suka rage.

Karin bayani