Sojojin bakin-daga sun soki Dasuki

Kanar Sambo Dasuki Hakkin mallakar hoto The Will
Image caption Kanar Sambo Dasuki

A Najeriya, sojojin da ke bakin-daga suna yaki da 'yan kungiyar Boko Haram sun kalubalanci mai bai wa shugaban kasar shawara kan tsaro, Kanar Sambo Dasuki a kan sukar da ya yi musu bisa kukan rashin makamai.

Daya daga cikin manyan jami'an sojojin a hira da BBC game da wadannan kalamai, ya bayyana cewar Kanar Dasukin maganganun da ya yi a London wurin yawansa na shakatawa, kamar yadda ya fada, ba su dace ba.

Babban jami'in -- wanda ya nemi a boye sunan sa -- ya ce su kadai ne da ke fafatawa da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka san bala'in da suke gani.

Ya ce maganganun da suka yi na rashin manyan makaman da za su fuskanci 'yan Boko Haram ba karya ba ne, saboda ko kasar Kamaru ta gaskata haka.

Babban Jami'in, ya kalubalanci Kanar Dasuki da cewar ai shi ma soja ne, ya sanya kakinsa ya ja ragama wajen kwato wasu yankuna da har yanzu suke hannun kungiyar ta Boko Haram.

Karin bayani