'Yan PDP ne suka kai hari a Bauchi - Yuguda

Image caption Yuguda ya ce manyan 'yan PDP ne suka sa aka kai hari a Bauchi

A Nijeriya gwamnan jihar Bauchi Malam Isa Yuguda, ya bayyana cewa 'yan jam'iyyarsu ta PDP ne suka kai hari kan taron yakin neman sake zaben shugaban kasar Goodluck Jonathan, amma ba 'yan jam'iyyar adawa ta APC ba.

A cewar gwamnan -- wanda shi ma dan jam'iyyar PDP ne -- wasu ne daga cikin manyan 'yan siyasa 'yan jam'iyyar ta PDP mai mulki 'yan asalin jihar ta Bauchi da ke Abuja, suka shirya tarzomar matasan.

Ministan Babban birnin tarayayya Bala Muhammad da shugaban jam'iyyar PDP na kasa Ahmadu Mu'azu dai na daga cikin kusoshin PDP 'yan jihar Bauchi da ake jin ba sa dasawa da gwamnan, duk da cewa jam'iyyarsu guda.

A ranar Alhamis ne wasu matasa suka kai farmaki kan taron gangamen na Shugaba Goodluck Jonathan a wasu tituna ciki har da lokacin da 'yan tawagar ke kan hanyarsu zuwa fadar sarkin Bauchi, da kuma a filin taron.