An hana lika fosta a jihar Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi Malam Isa yuguda
Image caption 'Yan adawa a jihar Bauchi sun ce ba za ta sabu ba, sai sun lika fastocinsu kamar yadda dokar Nigeria ta amince su yi.

Gwamnatin jihar Bauchi da ke arewacin Nigeria ta haramta lika fastocin 'yan takarar jam'iyyun siyasa a jihar.

Wannan mataki ya janyo cece-kuce da zazzafan martani musamman daga jam'iyyun adawa na jihar.

Sai dai gwamnatin ta ce ta dauki wannan mataki ne domin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al'umarta, tana mai cewa duk dan siyasar da ke son lika hotunansa to ya gina wurinsa na musamman ko kuma ya lika a ofishin yakin neman zabensa ko na jam'iyyarsa.

Gwamnatin ta kara da cewa manna hotunan barkatai kan haddasa tashin hankali ta yadda mutanen da babu ruwansu kan fada a tarkon tarzoma mai nasaba da hamayyar siyasa.

Amma a na su bangaren 'yan adawa a jihar Bauchi sun ce ba za ta sabu ba sai sun lika fastocinsu domin dokar Nigeria ta ba su damar yin hakan.