Girka:Jam'iyyar Siriza na kan gaba a zabe

Hakkin mallakar hoto EPA

Hasashen na nuna cewa jam'iyyar Siriza ta baiwa jam'iyyar 'yan mazan jiya mai mulkin kasar tazarar sama da kashi 12 bisa dari na kuri'un da aka kada.

Tuni dai magoya bayan jam'iyyar Siriza suka buge da murna suna shewa da wannan labarin ya same su a sakatariyar jam'iyyar

Dan takarar jam'iyyar Siriza, ya sha alwashin daidatawa da kasashen duniya wajen sauke wa kasar Girka nauyin bashin da ya yi mata kanta,

Yana mai cewa zai kawo karshen shirin gwamnatin kasar mai ci na tsuke-bakin-aljihun gwamnati, saboda a cewarsa Girka ba za ta iya biyan bashin ba, don haka a yafe mata.

Amma Firayim Ministan kasar, Antonis Samaras ya tsaya kan bakansa, cewa shirin tsuke-bakin-aljihun gwamnatin yana tasiri.