An fara kada kuri'a a kasar Girka

Shugabannin manyan jam'iyyun siyasar kasar Girka Hakkin mallakar hoto .
Image caption Kasar Girka ta fuskanci matsin tattalin arziki.

Al'umar kasar Girka sun fara kada kuri'a a Zaben gama gari, wanda zai iya sawa kasar ta yi kokarin sake yarjejeniyar da ta kulla da kasashen duniya game da basussukan da suka ba ta don ceto tattalin arzikinta.

Babbar jam'iyyar kasar Syriza mai ra'ayin sauyi da Alexis Tsipras ke jagoranta ta ce ta na son a yafe wani bangare na bashin, sannan a sassauta matakan tsuke bakin aljihu da aka dauka, wanda ya janyo radadi ga miliyoyin al'umar kasar.

Sai dai jam'iyyar New Democracy da ta dan karkata ga ra'ayin rikau, wanda Prime Ministan kasar Antonis Samaras ke jagoranta, ta ce tattalin arzikin Girkan na farfadowa a karkashin sabbin matakan da aka dauka, tare da gargadin cewa jam'iyyar Syriza ka iya tilastawa kasar Girka ficewa daga Tarayyar Turai.