Shugaban 'yan tawayen LRA zai gurfana a ICC

Shugaban 'yan tawayen LRA Dominc Ongwen
Image caption Ongwen tun ya na dan SHEKARU 10 ya ke cikin kungiyar 'yan tawayen LRA.

A ranar Litinin ne babban kwamandan kungiyar 'yan tawayen kasar Uganda Dominic Ongwen zai gurfana gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya da ke Hague.

Dominic Ongwen ya kasance babban kwamandan kungiyar 'yan tawaye ta Lord's Resistance Army ta kasar Uganda, kuma ana tuhumarsa ne da zarge-zargen aikata laifukan yaki.

A farkon wannan watan na Janairu ne aka kama shi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Babbar mai gabatar da kara ta kotun ICC, Fatou Bensuda, ta ce gurfanar da shi a gaban kotun ya kawo karshen kungiyar ta LRA, kuma ana gab da kawo karshen ta'addancinsu.

Ongwen dai na daya daga cikin shugabanni biyar da kotun ICC ta tuhuma shekaru goma da suka gabata.

Kungiyar LRA ta sace Ongwen tun yana dan shekaru goma a lokacin da yake kan hanyar sa ta zuwa makaranta a arewacin kasar ta Uganda.