John Kerry zai gana da Buhari da Jonathan

Sakataren harkokin wajen Amurka Hakkin mallakar hoto b
Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka

Yau, sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry, zai gana da 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP da kuma na APC a birnin Lagos.

Ana hasashen ganawar za ta karkata ne ga tattauna yadda za a kai zuciya nesa akan duk wani abu da zai nemi tayar da zaune tsaye a yayin kamfe da kuma shirin zaben shugaban kasa a Nijeriya - wanda za a gudanar a ranar 14 ga watan gobe.

Magoya bayan manyan jam'iyyun biyu suka kai farmaki ga juna a yakin neman zaben da suke yi tare da kalaman batanci da tsokanar fada.

Karin bayani