Boko Haram: AU ta bukaci a dauki mataki

Hakkin mallakar hoto
Image caption Rikicin Boko Haram zai kasance cikin batutuwan da taron kolin AU zai duba a ranar Juma'a

Kungiyar tarayyar Afrika, AU ta bukaci gwamnatocin kasashe a nahiyar su gaggauta daukar matakan dakile barazanar da kungiyar Boko Haram ke yi.

Shugabar kungiyar Nkosazana Dlamini-Zuma ta ce hare-haren da Boko Haram ke kai wa a kasashen ketare na nuni da hadarin da ke tattare da ayyukan kungiyar.

Najeriya dai ta yi watsi da tayin shiga tsakani da kungiyar ta AU ta yi mata bisa hujjar cewa dakarun yammacin Afrika kadai sun isa su yi maganin matsalar.

Shugabar wadda ke jawabi a taron ministocin nahiyar a Addis Ababa, ta ce hare-haren baya-bayan nan da Boko Haram ta kai na da ta da hankali matuka.