Kotu a Masar ta daure likita kan kaciyar mata

Image caption Hukuncin shi ne irinsa na farko a Masar

Wata kotun daukaka kara a Masar ta yanke hukuncin daurin sama da shekaru biyu ga wani likita bisa yi wa wata yarinya mai shekaru 13 kaciya, wadda ta mutu.

An daukaka karar ne bayan wata ta wanke Dr. Raslan Fadl a watan Nuwambar bara, abin da ya bai wa masu fafutuka takaici.

Ko da ya ke shekaru shida kenan da Masar ta haramta yi wa mata kaciya, amma har yanzu ana wannan al'ada.

Wadanda su ke fafutukar ganin an kawar da al'adar dai sun yi maraba da hukuncin kotun daukaka karar.