An saki 'ya'yan Hosni Mubarak daga kurkuku

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kama Gamal da Alaa ne shekaru hudu da suka wuce.

Wata kotu a Masar ta saki 'ya'yan tsohon shugaban kasar, Hosni Mubarak daga gida yari bayan sun kwashe kusan shekaru hudu a daure.

An sako Gamal da Alaa Mubarak ne da safiyar ranar Litinin.

An kama su ne tare da mahaifinsu bayan an hambarar da Mista Mubarak a farkon shekarar 2011 sakamakon bore na makonni da ake yi na kin jinin mulkinsa.

An tuhume su ne da cin hanci da rashawa, kodayake a makon jiya kotun ta bayar da umarnin sakin su har sai an sake yin shari'a game da batun.

Mista Mubarak na ci gaba da kasancewa a wani asibitin sojin kasar, inda yake a daure bayan an same shi da laifin almubazzaranci da dukiyar kasa.